Hukumar EFCC ta Damke Mata da Surukarta Bisa Zargin Zambar Makudan Kudi

Advertisement

Hukumar EFCC ta Damke Mata da Surukarta Bisa Zargin Zambar Makudan Kudi

 


Hukumar EFCC ta kama wata Blessing Nchelem da surukarta Deborah Jack bisa zargin zambar kudin wasu filaye da ba nasu ba akan N6m An kama su ne a birnin Port Harcourt da ke jihar Rivers da zargin zambatar Senibo Richmond Opusunju kan cewa za su sayar masa da filaye uku Mai shari’a P. I. Ajoku ta tisa keyarsu gidan gyaran hali da tarbiyya yayin da ta umarci lauyansu S. O. Aburu ya nemi beli a rubuce ba da baki ba Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi! A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Rivers- Hukumar hana yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati (EFCC) ta bayyana cafke wasu mata Blessing Nchelem da surukarta Deborah Jack tare da gurfanar da su gaban kotu. KARA KARANTA WANNAN "Ka da ka yi tunanin aure sai ka ajiye N50m," 'Yar Tiktok ta ba maza shawara An kama su a jihar Port Harcourt da ke jihar Rivers bisa zargin zambar kudin fili N6m, tare da gurfanar da su gaban babbar kotun tarayya karkashin mai shari’a P. I. Ajoku. An kama Blessing Nchelem da Deborah Jack bisa zambar N6m Hoto: Economic and Financial Crimes Commission Asali: Facebook EFCC da ta wallafa hakan a shafinta na facebook ta bayyana cewa ana zargin mutanen da kokarin damfarar wani Senibo Richmond Opusunju kudi N6m na kudin filayen uku da ba nasu ba. LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng Wane laifi EFCC take zarginsu da shi? Hukumar EFCC ta kama matan biyu bisa zargin zambar kudin filaye, tare da hada kai domin aikata laifi, karbar kudi ta hanyar zamba, da kuma adana kudin haramun da yawansu ya kai N6m. Da aka karanto musu laifuffukansu, matan sun musanta dukkanin zarge-zargen da ake yi musu, inda nan take lauyansu S. O. Aburu ya roki kotu ta bayar da belinsu, kamar yadda Punch ta wallafa. KARA KARANTA WANNAN Shugaban majalisa ya fadi muguwar illar da bukatar NLC za ta yiwa ma'aikata Amma lauyoyin EFCC sun nemi kotu da kada ta bayar da belinsu, a kuma Sanya ranar fara sauraron shari’ar tare da tisa keyarsu zuwa gidan kaso. Mai shari’a Ajoku ta ki bayar da belin mutanen biyu, sannan ta umarci lauyansu ya nemi belin a rubuce a zama na gaba. EFCC ta kama matashi a Gombe A wani labarin kuma kun ji cewa hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta damke wani matashi a jihar Gombe bisa zargin cin zarafin Naira. An cafko matashin ne bayan an gano shi yana lika N200 a wani gidan rawa, kuma EFCC ta tabbatar da sai ta hukunta da shi domin dakile faruwar haka a gaba. Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Post a Comment

0 Comments

on Freevisitorcounters.com