Shekara ta 10 dayin Aure Ina Fatan Allah Ya Kashe ni a Dakin Mijina – Fati Ladan

Advertisement

Shekara ta 10 dayin Aure Ina Fatan Allah Ya Kashe ni a Dakin Mijina – Fati Ladan

 Tsohuwar Jarumar Kannywood Fati Ladan ta bayyana irin Zaman Amana dasu kayi da mijinta har tsawon Shekara goma, Kuma tayi fatan Allah ya kashe ta a dakin Mijin ta.

Fati tayi waɗannan kalaman ne a hirar da tayi da manema labarai dangane da cikar ta shekara goma a gidan aure a gidan mijin ta dake a Jahar Kaduna. Alhaji Yerima Shettima, shine Mijinta Kuma shine Shugaban Ƙungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa (Arewa Youth Consultative Forum).

Fati da Mijinta Alhaji Shettima suna da Yaya biyu a tsakanin su, Aisha Humaira da Muhammad Shafi’u, kuma suna zaune ne a Kaduna. Fati ita ce amarya a cikin matan sa biyu.

Post a Comment

0 Comments

on Freevisitorcounters.com